Monday

Home › › Jonathan ya bayyana yadda 2018 ka iya zama alheri ga 'yan Najeriya
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya
bayyana abubuwan da ‘yan Najeriya ya
kamata su yi da zai sa shekara 2018 ya fi
shekara 2017 albarka.
Jonathan, 2018
Jonathan ya bayyana haka ne sakon sa na
shiga sabuwar shekara, inda ya shawarci 'yan
Najeriya su rika furta kalaman alheri akan
kasar da kuma kaunar juna.

“Duka mu muna kaunar Najeriya kuma muna
mata fatan alheri, duk da irin matsalolin da ta
ke fuskanta ba dai-dai bane mu rika furta
munanan kalamai akan Najeriya.

“Ya kamata mu rika fadan kalaman alheri
akan Najeriya. Idan muka yi haka, shekara
2018 za tafi shekara 2017 albarka musamman
idan muka yawaita yi mata adu'a masu kyau a
duk lokacin da muka tashi daga barci da safe.

“Ina rokon Allah ya biya wa duka yan
Najeriya bukatun su na alheri a cikin wannan
sabuwar shekara da muka shiga.
"Ina muku barka da shiga sabuwar shekara
sako daga tsohon shugaban kasa Goodluck
Jonathan (GEJ).
No comments:
Write Comments