Saturday

Home › › Kishin Kishin: Ana tunanin Sheikh Isa Ali Pantami zai tsaya takarar gwamnan Gombe.
Ana cigaba da rade-raden cewa shahararren malamin addinin islama din nan mai suna Sheikh Isa Ali Pantami zai tsaya takarar gwamnan jihar sa ta Gombe a zabe mai zuwa. Wannan dai na zuwa ne bayan da kiraye- kiraye ke dada kara yawaita daga jama'ar jihar da dama zuwa ga shugaban ganin cewa lokacin ya matso. NAIJ.com ta samu dai cewa a yayin daya daga cikin wannan kiraye-kirayen da ake yi masa, wani bawan Allah da ake kira da Malam Lawal Mu'azu Bauchi ya wallafa a shafin sa na Facebook, malamin ya mayar da martani. Sai dai a martanin malamin ya nuna matukar shakkun sa game da hakan inda ya nuna cewa yana tsoron shugabanci musamman ma na gwamna da yake da matukar girma. Haka nan kuma malamin ya bayyana cewa duk da haka akwai yiwuwar kowa ya bayar da gudummawar sa domin kawo cigaba mai ma'ana. SOURCE HAUSA.NAIJA.NG
No comments:
Write Comments