Tuesday

Home › › Shugaba Buhari zai Bude wasu Manyan Ayyuka da Ya Aiwatar a ranan Alhamis mai zuwa
Shugaba Buhari zai kaddamar da
wasu muhimman ayyuka a ranar
Alhamis mai zuwa.

- Zai kaddamar da wajen sauke kayan jirgi na
farko dake Kakuri, Kaduna.
- Ana sa ran wannan aiki da za’a kaddamar da
samar da akalla ayyukan yi 5000
- Har ila yau shugaban kasar zai kaddamar da
sababbin jiragen kasa 10

buhari zai, kaddamar

Rahotanni sun kawo cewa a ranar Alhamis, 4
ga watan Janairu, 2018 shugaban kasa
Muhammadu Buhari zai kaddamar da wajen
sauke kayan jirgi wato Nigeria's Inland Dry
Port na farko a Kakuri, jihar Kaduna.
Zai tarbi kayan jirgi daga tashar jiragen ruwa
na Apapa dake jihar Lagas, ta hanyar jiragen
kasa ko kuma mota.
ayyukan buhari
Sannan kuma ana sanya rai zai samar da
ayyukan yi akalla guda 5000.
2018 buhari buhari, buhari 2018
Har ila yau shugaban kasar zai kaddamar da
sababbin jiragen kasa guda 10 da kuma
injinan jiragen kasa guda biyu na hukumar
tashar jiragen kasa na Kaduna zuwa Abuja.

SOURCE FROM HAUSA-NAIG.COM
No comments:
Write Comments