Sunday

Home › › 'Yan Najeriya 14 da aka yankewa hukuncin kisa a Madinah sun aiko wa da Buhari sako
Wasu 'yan Najeriya su 14 da aka tura
kurkuku a Madinah ta kasar Saudiyya sun
aiko wa shugaba Buhari sakon neman
taimako domin ya kubutar da su daga wukar
hauni.

Ana tuhumar 'yan Najeriyan ne da tu'ammali
da miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya, kuma
kasar tana zartar da hukuncin kisa ne ga duk
wadanda suka aikata irin wannan laifi.
Saidai 'yan Najeriya sun tsorata bayan an
tura su gidan yari, suna masu cewar basu
aikata laifin ba kuma kasar ba zata yi masu
adalci ba.

"Mun san kashe mu zasu yi, muna rokon
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo
mana agaji, a duba tuhumar da suke yi mana
domin ba zasu bama damar kare kan mu ba."

Daga cikin 'yan Najeriya dake kurkukun
akwai: Lolo Babatunde, Biola Lawal, Hafis
Amosu, Jimoh Ishola, Tunde Ibrahim,
Abdurimi Aweda, Adam Abubakar, Amode
Tunde, Adewumi Adepoju, Saka Riyau, Aliu
Muhammed, Abdul Raman, Yekini Yahaya da
kuma wasu mata guda biyu. Akwai karin
wasu 'yan Najeriya dake gidajen yari a
Riyadh da Makkah a kasar Saudiyya.

Wadanda ake tuhumar sun tuntubi ofishin
jakadancin Najeriya dake Riyadh da kokon
barar a taimake su kafin kasar ta Saudiyya ta
zartar masu da hukuncin.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewar
tana da masaniyar daurin 'yan Najeriya a
kurkuku a kasar Saudiyya bisa zarginsu da
tu'ammali da miyagun kwayoyi. Minista
harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama,
ya tabbatar da cewar gwamnatin Najeriya na
daukan matakan da ya dace domin
tattaunawa da hukumomin kasar Saudiyya a
kan makomar 'yan Najeriyan.

SOURCE : @HAUSA.NAIJA.NG
No comments:
Write Comments