Sunday

Home › › Abinda Shugaban jam'iyyar PDP da IBB suka tattauna a ganawar su ta jiya
Tun bayan zungureriyar budaddiyyar wasikar da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya aikewa shugaba Buhari a kan ya hakura da batun tsayawa takara a zaben 2019, 'ya'yan jam'iyyar PDP ke tururuwar zuwa gidansa domin kulle-kullen siyasa dangane da zaben shekarar 2019.

A jiya, Asabar, shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya jagoranci shugabannin jam'iyyar zuwa gidan IBB dake garin Minna a jihar Naija a wata ziyarar ban girma.
Shugabancin jam'iyyar PDP ya dira garin Minna domin ganawa da IBB
Wata majiya dake da kusanci da IBB ta shaidawa jaridar Daily Trust cewar Secondus ya yiwa IBB bayani a kan irin kokarin da jam’iyyar PDP ke yi domin kai wag a nasara a zaben shekarar 2019.
Majiyar ta rawaito cewar Secondus na bugun kirjin cewar jam’iyyar PDP a shirye take dangane da zaben 2019, tare da bayyana cewar in dai don PDP ne ko yanzu a fito a buga zabe.

IBB ya bayyana jin dadinsa da ziyarar da kuma irin yadda jam’iyyar ke aiki tukuru domin karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC tare da jaddada goyon bayansa ga jam’iyyar.

Babangida ya nanata imaninsa ga zaman Najeriya a matsayin kasa daya mai kabilu daban-daban tare da yin kira ga shugabnnin jam’iyyar da su tabbatar da hadin kai da zaman lafiyar Najeriya.
Saidai, a yayin da IBB ke ganawa da shugabancin jam'iyyar PDP, shugaban jam'iyyar APC, John Oyegun, ya karbi dubban magoyan bayan jam'iyyar PDP da suka canja sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jiyan, Asabar.
Daga cikin wadanda suka canja shekar akwai tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP a jihar, Aminu Yusuf, tsohon shugaban majalisar jihar, Adamu Usman, da tsohon alkalin alkalai, Abdullahi Wuse, kamar yadda naij.com ta kawo maku a daya daga cikin labaranta.
No comments:
Write Comments