Wednesday

Home › › Sace yan makaranta: PDP ta nemi Buhari ya tafi Dapchi
Rahotanni sun kawo cewa babban jam’iyyar adawa PDP ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tattara kayansa ya koma garin Dapchi domin ya gano mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ta sace.

A wani jawabi daga mai magana da yawun jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa:
"PDP na son Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shakatawar da yake yi da jam'iyyar APC a fadar Aso Villa ya nuna yadda ake shugabanci ta hanyar tafiya Dapchi da ke Yobe, domin samun labari da zafinsakan abin da ya sa aka sace mata 'yan makaranta 110 yana ji yana gani".

Haka zalika PDP ta ce abin kunya ne ga shugaban kasar da jam'iyyarsa ta APC su rika biki da shirin zaben 2019 a fadarsa a lokacin da iyayen 'yan matan ke juyayin rashin ganin 'ya'yansu.

A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka ta shigar da sunan jagoran wani tsagi na Boko Haram, Abu Musab Al-Barnawi cikin jerin gagga gaggan yan ta’addan da kasar ke sanyawa ido tare da nemansu ruwa a jallo.

Jaridar The Cables ta ruwaito ana zargin Abu Musa’ab Al-Barnawi da satar daliban kwalejin yan mata dake garin Dapchi na jihar Yobe a cikin satin daya gabata, wanda a shekarar da ta gabata ISIS ta sanar da shi a matsayin shugaban Boko Haram.

SOURCE @hausa.naija.ng
No comments:
Write Comments