Tuesday

Home › › Tirƙashi: Ma'aurata sun yi cinikin jaririyar su awanni ƙalilan bayan haihuwar ta
Bayan gudanar da bincike na tsawon makonni uku, hukumar 'yan sanda ta jihar Imo, ta yi ram da wasu ma'aurata da suka sayar da jaririyar su kan kudi N400, 000 bayan awanni kadan da haihuwar ta.
Wannan ma'aurata 'yan asalin jihar Abia, Ifeanyi da kuma Emmaculata Elijah, 'yan asalin garin Amakpu ne a karamar hukumar Isiala Ngwa ta Arewa.

A ranar Litinin din da ta gabata ne, hukumar ta gurfanar dasu ne a babban ofishin ta dake birnin Owerri, inda kakakin 'yan sandan, Andrew Enwerem ya bayyana cewa, wannan miyagu sun aikata lafin ne a ranar 26 ga watan Janairu bayan awanni kalilan da haihuwar 'yar ta su.


Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wannan mutane sun tarayya da wasu 'yan uwan su wajen aikata laifin, inda suka sayarwa da wannan jaririya ga wani mutum da sunan Obiekwe.

Enwerem ya ci gaba da cewa, wannan ma'aurata sun haifi yara bakwai amma har yanzu babu masaniyar inda 'ya'yayen su biyu suka shiga.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, a ranar 17 ga watan Fabrairu ne aka gano wannan jaririya a birnin Legas, inda kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Imo, Chris Ezike ya bayar da umarni na gaggawar kammala bincike domin gurfanar da wannan miyagu a gaban alkali.
No comments:
Write Comments