Wednesday

Home › › Wani mutum yayi alkawarin bawa duk wani wanda yayi rijistar zabe Kudi :: karanta
A kokarinsa na kara wa jama'arsa da
yankinsa tagomashin siyasa, wani mutum
daga kabilar Ibo, ya sha alwashin rabok kudi,
Naira dubu-dubu, ga duk wani wanda ya
garzaya yayi rajista a ofishin hukumar INEC,
daga shiyyar kudu maso gabas.

Su dai kabilun Ibo, wadanda suke ganin
kamar ana zaluntar su, kuma ana musu
wariya, tun zamanin mulkin basasa, har
yanzu, basu yo siyasar tsakiya ba, inda
kullum basu iya hada kai su dunkula
kuri'unsu wuri guda.

A wannan karon, ga alama sun farka, ganin
yadda suke ta kayya-kayya a yanar gizo kan
ko su balle ko su bata wa shugaba Buhari
suna, musamman ganin ya kayar musu da
dan-gida Ebele Jonathan.

A jaddawalin shiyyoyin Najeriya dai da aka
fitar, yankin kudu maso gaban din na Igbo,
shine mafi kankantar jama'a wadanda suka
yi rajista domin shiga zabuka su kada quri'u
a badi.


Shiyyoyin, sun hada da arewa ta tsakiya, ta
gabas da ta yamma, kudu maso kudu, maso
yamma ta Yarabawa da ta gabas.
No comments:
Write Comments