Saturday

Home › › Zamu Fitar da Dan takara da Bai-kai Buhari shekaruba : Shettima Yarima
Yayin da farfajiyar siyasa ke dada kara dumama
tare da daukar sanyi, shugaban tuntuba na
matasan arewacin Najeriya Alhaji Shettima
Yerima ya bayyana kudurin su na fitar tare da
marawa dan takara daga Arewa baya da bai kai
shugaba Buhari yawan shekaru ba.
2019 buhari, shettima yarima
Alhaji Shettima ya bayyana cewa cikin
abubuwan da suka sa har yanzu kasar
Najeriya ke ta fama da tarnaki musamman ta
fuskar siyasa hadda tsufan da shugaba Buhari
ke fama da shi.

Jaridar NAIJ.com ta samu cewa daga nan ne sai
shugaban matasan ya bayyana cewa matasa
daga arewacin kasar za su koma bisa teburin
nazari su kuma yi karatun ta-natsu sannan
su fitar da dan takarar da za su marawa baya
a zaben 2019.
No comments:
Write Comments