Saturday

Home › › Allah buwayi: An haifi jaririya mai hannaye 4 da kafafu 3 a garin Kaduna
Kamar dai yadda muka samu, wani abun al'ajabi da ba kasafai ake samu ba ya auku a garin Kaduna dake a arewa maso yammacin kasar nan bayan da wata mata mai suna malama Hauwa'u Jamilu mai shekaru 24 a duniya ta haifi 'yan biyu duka mata amma daya na da hannaye 4 da kafa 3.
Malama Hauwa'u dake zaman matar malam Kabiru dake sana'ar Kafita, ta dai haihu gida ne kamar yadda muka samu a ranar Lahadin da ta gabata, ta watan jiya.


To sai dai da take yiwa majiyar mu ta Daily trust bayani, mahaifiyar jaririyar ta bayyana cewa ikon Allah ne kuma ita hankalin ta a kwance yake domin diyar ta ce kuma tana son abun ta.
Bayan ganin irin hallitar jaririyar dai iyayen ta sun kai ta asibiti inda daga nan kuma aka aike da ita babbar asibitin koyarwa na jami'ar Bauchi wadanda suka bayar da tabbacin za'a iya yi wa jaririyar aiki.

Haka ma dai Mun samu labarin cewa wata mata hatsabibiya maras imani ta sadada ta shiga asibitin gwamnati mallakin jihar Kaduna na Dantsoho ta kuma sace jariri, sabuwar haihuwa na wata mata kurma mai suna Salamatu Kabir.
Kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta Daily trust, an haifi jaririn ne a ranar 10 ga watan Janairun da ya gabata amma sai kuma ya bace sama-ko-kasa a ranar, kimanin awa daya kacal bayan haihuwar ta sa.
No comments:
Write Comments