Monday

Home Karanta : Ko kun san wacece Hajiya Zainab, tsohuwar matar Dangote?
 Hajiya Zainab itace mahaifiyar Amarya Fatima
Dangote da ta yi aure satin da ya wuce
Tabbas shahararren mai kudin nan na daya a dukkan nahiyar Afrika dan asalin garin
Kano, Alhaji Aliko Dangote mutum ne mai
matukar kankan da kai da kuma kokarin
boye rayuwar iyalin sa, hakan ne ma ya
sanya ba kowa ne yasan ya rayuwar ta su take ba.
Sai dai daman Hausawa na cewa ranar
wanka, ba'a boyon cibi don kuwa yanzu
bayanai da ya wa sun fita a bainar jama'a
inda aka fahimci cewa shi Dangote din ya
taba yin aure a baya, ya kuma rabu da matar
ta sa watau mahaifiyar amarya Fatima
Dangote kenan da ta yi aure a kwanan baya.
NAIJ.com ta samu cewa a wurin bikin ne ma
jama'a suka fara ganin tsohuwar matar ta sa
mai suna Hajiya Zainab a inda ta ke gaba-
gaba wajen shirin bukukuwan da aka
gudanar.
Yawancin mutane dai da sun ga mahaifiyar
amaryar za su iya fahimtar hakan ko ba tare
da tambaya ba domin irin kamar da suke yi
sosai.
A baya ma dai mun kawo maku cewa mijin
Fatima din Jamilu shine babban da ga
mahaifin sa, tsohon shugaban 'yan Sanda
Muhammad Dikko Abubakar, wanda yanzu
haka an fara shagalin biki sa da amaryar ta
sa.
Shi dai Jamilu matashin mai kudi ne kuma
yana da sunan gayu da ake kiran sa dashi a
cikin abokan sa wato 'Jamboy' wanda kuma
hakan ne yake rubuce a jikin lambar motocin
sa na alfarma da. SOURCE @HAUSA.NAIJA.NG
No comments:
Write Comments