Sunday

Home › › Magidanci a Indiya ya watsa wa matar sa guba don ta haifi mace.
Wani mutum mai suna Siraj mai shekaru 32, ya watsa ma matarsa mai suna Fara mai shekaru 25, guba wato acid tana cikin bacci saboda ta haifar masa diya mace shi kuma namiji yakeso. Tayi mummunar kuna a sakamakon gubar da Siraj, wanda aka fi sani da Bhura ya zuba mata tana cikin bacci, a garin Moradabad kusa da New Delhi, a ranar Litinin kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito. Yace bata biyashi ladan sadakinta daya biya ba tunda bata haifa masa namiji ba. Mutumin ya ja mata munanan raunuka a jiki wanda yasa jami’an ‘yan Sanda suka shiga farautarsa. An hanzarta kai Farah asibitin karkara sokamakon mummunan halin da ya jefata, inda ta samu kuna a Fuska, hannuwa, da kuma ciki. Ma'aauratan dai sunyi shekara takwas tare kuma suna da yara biyu duk mata. SOURCE @HAUSA.NAIJA.NG
No comments:
Write Comments