Saturday

Home › › Dandalin Kannywood: An kafa kwamitin mutane 28 don tsaftace harkar fim
Labarin da muke samu na nuni ne da cewa
wasu manyan masu ruwa da tsaki a
harkokin finafinan Hausa ta Kannywood
sun kafa wani kwamiti mai mutane ashirin
da takwas da aka dorawa alhakin bincike
tare da gano matsalolin da masana'antar ta
ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin da za
a bi domin a magance su.

Wannan kwamitin dai kamar yadda
muka samu, ya tattara masana daga
dukkan bangarorin da dama daga cikin
masu gudanar da sana'ar ta fim.

NAIJ.com har ila yau ta samu cewa
Malam Bashir Mudi Yakasai ne aka
baiwa shugabancin kwamitin yayin da
kuma Sakataren kwamitin ya zama
Malam Ahmad Abubakar.

Ga dai sunayen 'yan kwamitin nan:


1. Bashir Mudi Yakasai - Shugaban
kwamiti
2. Ahmad Abubakar - Sakataren
kwamiti
3. Baballe Hayatu
4. Aisha Aliyu Tsamiya
5. Sunusi Oscar
6. Hauwa Waraka
7. A.A. Rasheed
8. Shehu Hassan Kano
9. Bilkisu Yusuf Ali
10. Sani Sule Katsina
11. Habib Barde
12. Jamila Nagudu
13. Muhammad Gumel - Ma'ajin
kwamiti
14. Ibrahim Mandawari
15. Nasir B. Muhammad
16. Sani Rainbow
17. Haruna Talle Maifata
18. Ruƙayya Dawayya
19. Misbahu M. Ahmad
20. Kabiru Shugaba
21. Salisu Mu'azu
22. Rahama Abdulmajid
23. Al-Amin Ciroma
24. Salisu Muhammed Officer
25. Bala Kufaina
26. Umar Sani UK
27. Ali Jita
28. Aminu S. Bono

Source:@Hausa.naija.ng
No comments:
Write Comments