Tuesday

Home Gwamnatin tarayya ta gwangwaje matasan yankin Naija-Delta 90 da tallafin N500,000 ga kowannensu
Kowanne matasshi daga cikin matasa 90 a yankin Naija-Delta ya karbi tallafin N500,000 domin fara sana'ar dogaro da kai.
An bawa matasan kudin ne a matsayin jari domin fara sana'a a bangaren noma da wasu sana'o'i da aka bawa matasan horo a kai a karkashin ma'aikatar kula da al'amuran yankin Naija-Delta. Ministan ma'aikatar kula al'amuran yankin Naija-Delta, Usani Usani, ya bukaci matasan da su yi amfani da kudin da gwamnatin tarayya ta daba masu ta hanyar da ta dace. Gwamnatin tarayya ta gwangwaje matasan yankin Naija-Delta 90 da tallafin N500,000 ga kowannensu Usani Uguru Usani Kazalika, Ministan, ya yi kira ga mata da matasa a yankin da su yi amfani da damar koyon sana'o'in dogaro da kai da gwamnatin tarayya ta kirkiro domin inganta rayuwar su. Ministan, da Ediomu Ebioghe Philip; babban sakatare a ma'aikatar, ya wakilta, ya ce, babban burin ma'aikatar shine tallafawa mata da matasa domin rage radadin fatara da talauci. "Ina mai baku shawarar ku yi amfani da kudin da aka baku ta hanyar da ya dace, ta hanyar kafa wata sana'a da zata zamar maku silar arziki a tsawon rayuwar ku ta duniya," a cewar Mista Philiph. Sannan ya kara da cewar, shirin bayar da tallafin zai cigaba tare da bawa matasan tabbacin cewar da yawa zasu ci moriyar tsarin a gaba. Matasan da suka ci moriyar tsarin sun fito be daga jihohin Akwa Ibom, Abiya, Bayelsa, Kuros Riba, Delta, Imo, Ribas, da kuma Ondo.
No comments:
Write Comments