Tuesday

Home Buhari Ya Jajantawa Al'ummar Filato : Bayan Asarar Rayuka Da Ya Faru A Garin
Jaridar Premium Time ta kasar nan ta bi diddikin abin da ya faru har ta kai rikici ya barke tsakanin Fulani da ‘Yan kabilar Birom a Garin Barkin Ladi da ke cikin Jihar Filato a karshen makon jiya.
Shugaban Kasa Buhari ya jajantawa mutanen Filato.

Bincike ya nuna cewa kafin Ranar Asabar din da aka yi wannan kashe-kashe an hallaka wasu Fulani har 4 yayin da su ke dawowa daga wata kasuwar kara ta dabbobi a Garin Bukuru. Hakan ne ya jawo wasu Fulani su ka tashi su ka dauki fansa.

Wani Shugaban Fulani na Kungiyar su ta Miyetti Allah da ke Yankin Danladi Ciroma ya tabbatar da cewa ‘Yan kabilar Birom din sun kona mutanen su kurmus da ran su sannan kuma sun yi gaba da shanu sama da 300 na Fulanin da ke Yankin kafin nan.
Bayan wannan abin takaici ya faru ne wasu Fulani su ka shirya su ka kai wa ‘Yan Birom din hari. Su kuma dai ‘Yan kabilar Birom din sun yi ramuwar gayya daga baya inda su ka rika tare mutane a hanya su na kashe duk wadanda ba Mabiya addinin Kirista ba.Daga cikin Fulanin da aka kashe akwai Bala Adamu, Isa Mohammed, Ibrahim Ahmed da Lawal Abubakar Dangana. A jiya dama kun ji cewa Jami’an tsaro dai sun tabbatar da cewa rikicin yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 86 a tashi guda a Jihar.
No comments:
Write Comments