Sunday

Home Arsenal tayi Gwanjon 'yan wasa 12 ciki har da Cazorla da wilshere
Ƙungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta bayyana cewa yan wasanta Jack Wilshere da Santi Cazorla tare da wasu yan wasa goma zasu bar kungiyar a farkon wannan kakar wasannin ta bana. 

Ya zuwa yanzu dai kungiyar ta sayo 'yan wasa har guda uku tare da tsawaita kwantiragin wasu guda biyu.

Jack Wilshere mai shekaru


 26 da haihuwa ya fara ta ka ledarsa ne a kungiyar Arsenal tun yana karamin yaro inda ya shafe shekaru goma a kungiyar. 

Sai dai mai horas da sabuwar kungiyar Unai Emry ya bayyanawa dan wasan cewa ba zai samu damar buga wasanni da dama ba kamar yadda yake bukatar ya kasance daya daga jigon kungiyar.

Hakan yasa dan wasan rage kwantiraginsa domin neman mafita tare da sauya kungiya.
Shi kuwa Satin Cazorla zai bar kungiyar ne bayan da ya shafe kakar wasanni biyu yana jinyar raunin da samu. Dan wasan dan kasar Andulus bai sake taka leda ba tun a Oktoban shekara ta 2016. 

Yanzu haka dai ya fara atisaye a kungiyar Kwallon kafa ta Villarreal dake gasar Laliga ta kasar Spain.

Ragowar yan wasan da za’a sallama sakamakon karewar kwantiraginsu a kungiyar sun hada da:

1- Marc Bola

2- Santi Cazorla

3- Alex Crean

4- Vlad Dragomir

5- Aaron Eyoma

6- Yasin Fortune

7- Ryan Huddart

8- Chiori Johnson

9- Hugo Keto

10- Per Mertesaker

11- Tafari Moore
No comments:
Write Comments