Thursday

Home EFCC ta biyo ta kan Sirikin Obasanjo
Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a jihar Legas ta ingiza keyar wani babban dan kasuwa mai suna John Abebe zuwa gidan yari na Ikoyi kafin ta saurari korafin neman bayar da shi beli daga lauyansa.

Har ma alkali ya sa a tura shi gidan maza ya fara karbar gabza.
John Abebe wanda ya kasance kani ne ga marigayya Stella Obasanjo tsohuwar matar shugaban kasa Obasanjo, ya tsinci kansa ne a gaban kotun bisa zarginsa da laifin damfara.

Tun farko dai hukumar yaki da masu
yiwa tattalin arzkin kasa zagon kasa
(EFCC) ce ta gurfanar da shi bisa
tuhumar aikata laifuka shida dake da
alaka da damfara.

EFCC dai ta ce tana zarginsa ne da kitsa zaren wata harkyalla a wata wasikar da ya rubuta daga kamfanin BP Exploration Nigeria Limited mai dauke da kwanan watan ranar 30 ga watan Nuwamba 1995 zuwa Inducon (Nigeria) Limited.

Kana kuma hukumar na zarginsa da
yunkurin gujewa kamawa ta hanyar
shigar da kara yana mai kalubalantar
zargin da EFCC ke masa ta hanyar shigar da kara a kotu, hukumar ta bayyana lamba fayal din karar da ya shigar da ‘FHC/L/CS/224/2010’.
Sannan hukumar ta EFCC na sake
zarginsa da yunkurin yaudarar kotun ta hanyar gabatar da shaidar karya, wanda hakan ya saba da sashi na 120(2) na kundin manyan laifuka ta Cap C17 na jihar Legas na shekara ta 2003 kamar yadda lauyan EFCC Rotimi Oyedepo ya shaidawa kotun.
Amma sai dai wanda ake karar ya
musanta zargin, wanda hakan ta sanya mai shari’a Mojisola Dada ta saita masa hanyar zuwa kurkuku, sannan ta dage karar domin bawa lauyansa Uche Nwokedi (SAN) damar shigar da neman karbar belin wanda yake karewa.
No comments:
Write Comments