Thursday

Home Shekarau ya gindayawa Kwankwaso sharadin zaman lafiya
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam
Ibrahim Shekarau ya yi wa takwaran sa duk dai a jihar, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso maraba da dawowar sa jam'iyyar PDP tare. 

Sai dai kuma Shekaru din ya bayyana
cewa dole ne Kwankwaso yayi biyayya ga jagororin jam'iyyar a jihar idan dai har yana so ya samu zaman lafiya da salama.

NAIJ.com ta samu cewa Shekarau din wanda yayi magana ta bakin mai taimaka masa ta bangaren yada labarai, Sule Ya'u Sule, ya ce suna fatan dai Kwankwason ya canza halin sa kuma zai daratta duk shugabannin jam'iyyar da ya tadda.
No comments:
Write Comments