Sunday

Home › › Abin Da Buhari Ya Fada Akan Murabur Da Maman Taraba Ta Yi.
A jiya, Asabar, ne tsohuwar ministar harkokin
mata, Sanata Aisha Jumma Alhassan, ta sauya
sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress
(APC) zuwa jam’iyyar United Democratic Party
(UDP).

Inda a yau ne kuma bayan dawowar shugaba Buhari daga kasar Amurka inda ya halarci taron a majalisar dinkin duniya ya karbi takardar murabus din da tsohuwar ministar ta rubuta.
AISHA ALHASSAN (MAMAN TARABA)

A takarda da shugaba Buhari ya saka wa hannu
da kansa, shugaban kasar ya ce, " Na karbi takardar murabus dinki daga mukamin ministar mata ta Najeriya.

Na amince da murabus dinki ba tare da bata lokaci ba. "A madadi na da gwamnati da jama'ar Najeriya, muna yi maki godiya da irin gudunmawar da ki ka bayar ga kasa .

Tuni shugaba Buhari ya umarci Hajiya Aisha
Abubakar, karamar ministar raya masana'antu
da saka hannun jari, ta saka ido a harkokin
ma'aikatar mata.

Sanata Jummai wacce akafi sani da Mama Taraba ta yi murabus daga kujeran minister da shugaba Buhari ya nada ta saboda hanata takarar kujeran gwamnan jihar Taraba da jam’iyyar APC tayi.

A sakatariya jam’iyyar UDP, Jummai Alhassan ta
bayyana cewa ta fita daga jam’iyyar APC ne
saboda rashin adalci da akayi mata.
No comments:
Write Comments