Sunday

Home Kungiyar Kasashen Turai Zata Sanya Ido Kan Zanben Cikin Gida A PDP
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewar zata fitar da dan takarar shugaban kasa da duk 'yan jam'iyya da 'yan kasa zasu aminta da shi.

PDP zata gudanar da zaben fitar da dan takarar
shugaban kasa a garin Fatakwal, jihar Ribas,
ranar 6 da 7 ga watan Oktoba.


Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya
shaidawa manema labarai a jiya, Asabar, cewar
jam'iyyar na iya bakin kokarinta domin ganin ta
gudanar da zaben fitar da dan takarar cikin
nasara.

Ologbondiyan ya yi zargin cewar jam'iyyar APC
mai mulki na kokarin haddasa rikici a cikin
jam'iyyar. Amma ya ce PDP ba zata bari wani
abu ya hana ta yin nasara ba.

" Zamu gudanar da taron gangami cikin nasara kuma ba tare da rabuwar kai ba kuma zamu fitar da dan takarar da duk 'yan Najeriya zasu karbe shi hannu biyu.

"Kungiyar kasashen Turai (EU) ta nuna sha'awar saka ido a zaben mu na cikin gida. Muna iya bakin kokarinmu don gudanar da sahihin zabe na adalci.

"Za a nuna taron kai tsaye a gidajen talabijin, " a cewar Ologbondiyan. Ya kara da cewar PDP ba zata bari wani mutum ya yi kokarin juya akalar taron domin bawa wani dan takara fifiko ba.

Za a gudanar da zaben fitar da dan takarar ne
tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa,
Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Kano, Sanata
Rabi'u Musa Kwankwaso, shugaban majalisar
dattijai, Sanata Bukola Saraki, gwamnan jihar
Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, tsohon
shugaban majalisar dattijai, Sanata David Mark,
tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang da
tsohon minista a gwamnatin Jonathan, Tanimu
Turaki.
No comments:
Write Comments