Friday

Home "Yan Ta'adda Sun Kai Hari A Sakatariyar PDP Dake Bayelsa.
A ranar Alhamis ne wasu da ake kyautata zaton
'yan ta'adda ne suka tayar da hankulan
al'ummar Brass Island da ke jihar Bayelsa, inda
suka kai hari a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke a
yankin tare da kuma bude wuta akan jami'an
tsaro dake yankin.
Wannan yazo ne gabanin kai wani mummunan
hari da yan ta'adda suka yi ga dan takarar
majalisar wakilai ta tarayya karkashin jam'iyyar
APC a jihar Ondo, Mr Olatayo Aribo, inda suka
cinnawa daya daga cikin motocin yakin zabensa
wuta.


Dangane da ta'addancin Bayelsa kuwa, an samu
katsewar harkokin kasuwanci da sauran hada-
hadar yau da kullum bayan da magoya bayan
jam'iyyar PDP da ke a yankin da lamarin ya
shafa suka gudu daga gidajensu a safiyar
Alhamis don tsira da rayukansu.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan da
suka kunshi gungun mutane 5, karkashin uban
dabar Aboye, sun fito ne daga jihar Rivers, inda
suka fatattaki mazauna yankin a safiyar ranar
Alhamis.

An bayyana cewa sun yi harbe harben kan mai
uwa da wabi don tosrarta da jama'a kafin daga
bisani suka kai wa sakatariyar harin.
Da su ke jawabi ga manema labaria a garin
Yenagoa a ranar Alhamis, shugaban riko na
karamar hukumar Brass, Victor Isaiah;
mataimakin kakakin majalisar dokoki ta juhar,
Abraham Ingobere; da kuma sanata mai wakiltar
Bayelsa ta Kudu a majalisar dattijai, Ben Murray-
Bruce, sun yi Allah wadai da wannan harin.
Sun yi zargin cewa yan ta'addan sun kai wannan
mummunan harin ne bisa umurnin jam'iyyar
hamayya ta APC da ke a yankin.
Sun yi kira ga Sifeta Janar na rundunar yan
sanda da sauran jami'an tsaro da ke a jihar da su tashi tsaye haikan don kare rayuka da dukiyar
al'ummar yankin daga hare haren 'yan bangar
siyasa a jihar.
No comments:
Write Comments