Tuesday

Home Adams Oshiomhole ya zama Ala-ka-kai a Cikin APC : Cewar tsohon mai ba Jonathan shawara
Yanzu haka dai abubuwa na neman cabewa a APC watanni 4 rak da hawan Adams Oshiomhole kan kujerar Shugaban Jam’iyyar na kasa. Reno Omokri yace Adams Oshiomhole ya zama irin yadda Ali Modu Sheriff ya taba zama a PDP. Rigingimu sun barke a APC ne bayan zabukan da aka yi na fitar da gwani a watan jiya wanda hakan ya sa wasu Gwamnoni su ka huro wuta su na neman ayi waje da Shugaban Jam’iyyar na kasa. Reno Omokri yace dama ya san za a rina. A shafin na Reno Omokri yace banbancin Ali Sheriff wanda ya taba zama Shugaban PDP a baya da Adams Oshiomhole a APC shi ne, PDP tayi wuf ta kori Ali Sheriff kafin a fara shirin zaben 2019 yayin da ita kuwa APC ta kai gargara. Fasto Reno Omokri dai yace yanzu APC ta shiga uku domin kuwa ana daf da zabe yayin da shuganannin ta ke rikici. PDP dai kuma a wani bangaren ba ta fama da rikici na cikin gida yayin da aka dumfari babban zabe na kasa na 2019.
 
SOURCE : LEGITNG
No comments:
Write Comments