Wednesday

Home Amaechi : "Yan Nageriya Zasu Fara Shan Wutar Awa 24 Dazarar Zugaba Buhari Ya Koma.
Tsohon gwamnan jahar Ribas, shugaban yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa idan har gwamnatin shugaba Buhari ta zarce za’a fara samun wutar lantarki ta awa ashirin da hudu a Najeriya.


Amaechi ya bayyana haka ne a ranar Laraba 3 ga watan Oktoba a yayin daya zayyano ayyukan alkairin da yace gwamnatin Buhari ta dabbaka a Najeriya.

Amaechi yace gwamnatin Buhari ta ciri tuta wajen habbaka lamarin tsaro, gine ginen hanyoyi, yaki da rashawa, inganta harkar noma da kuma harkar abinda ya shafi sufuri, haka zalika Buhari bai yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da yan bindigan Fulani makiyaya. “A yanzu haka an samu cigaba adadin wutar da ake samarwa a Najeriya, daga mega watta dubu uku, zuwa mega watta dubu bakwai, amma megawatt dubu biyar kawai zamu iya rarrabawa saboda akwai wasu kayan aikin da suka lalace, amma a hankali muna gyarasu. “Tsarin shine mu samar da wutar awanni ashirin da hudu, amma har yanzu akwai gibin da bamu kammala cikewa ba, don haka idan muka zarce, zamu cike wannan gibi kuma wuta zai tabbata. Kuma ta abinda ya shafi yaki da rashawa kuma, ai da Buhari yazo cewa yayi kada kowa ya saci kudi, amma idan har ka sata tabbas zaka fuskanci hukunci. “Duk wanda yace ma’aikatar ayyuka ba ta aiki bai mata adalci ba, saboda akwai hanyar Bonny wanda aka watsar da ita tun bayan Obasanjo, amma zuwanmu sai gashi mun dauki gabarar gudanar da aikin duk da cewa kudin aikin ya karu.” Inji Amaechi. 

No comments:
Write Comments