Monday

Home Buhari Bai Isa Ya Hanani Fita Daga Nigeria Ba : Cewar Bafarawa
Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya nemi ayi maza a cire sunan sa daga wadanda aka haramtawa barin Najeriya saboda zargin satar dukiyar Gwamnati a lokacin su na kan mulki. Tsohon Gwamna na Sokoto yace babu Kotun da ke binciken sa a halin yanzu domin tuni an wanke sa. Attahiru Bafarawa yace sai da aka yi fiye da shekaru 10 ana shari’a da shi a Kotu kuma har ta kai a karshe an gane bai da laifin komai. Bafarawa a lokacin da yake wata hira da ‘Yan jarida jiya Ranar Lahadi, ya fadi cewa Shugaba Buhari bai isa ya hana sa fita daga Najeriya da sabon kudirin da ya kawo mai lamba ta shida E06 wanda za ta haramtawa wasu barin kasar nan. 

Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa tun farkon 2018 ne Alkalin wani babban Kotu ya wanke sa daga zargin da ke kan sa kuma har gobe babu kayan sa da Kotu ta karbe domin ba a same shi da aikata rashin gaskiya ba a gaban shari’a. Jiya dai kun ji Fadar shugaban kasa ta musanta rahoton dake yawo na cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari ta hana wasu manyan mutane har 50 fita daga Najeryiya saboda tuhumar da ke kan su a Kasar, 

No comments:
Write Comments