Friday

Home DSS : Nadin Yusuf Magaji Bichi Zai Kawowa Buhari Tangarda.
Nadin Yusuf Magaji Bichi da shugaba Buhari ya yi a matsayin sabon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ya bar baya da kura.

A yanzu dai wasu daga cikin manyan jami'an hukumar DSS da nadin Bichi bai yiwa dadi ba, na kulle-kullen ganin yadda zasu yi amfani da karfin su tare da gogewarsu ta aiki wajen ganin sun yiwa yunkurin Buhari na tazarce kafar ungulu tare da lalata duk wani yunkuri na kawo karshen yaki da Boko da gwamnatin ta Buhari ke yi.

A ranar 13 ga watan Satumba ne Bichi ya karbi aiki daga hannun shugaban DSS na rikon kwarya, Matthew Seiyefa, mutumin da ya zama shugaba a hukumar bayan Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki. 


Manyan jami'an DSS dake shelkwatar su dake Abuja da abokanan aikinsu dake jihohi sun fusata da nadin Bichi ne saboda ganin cewar ya riga ya yi ritaya amma shugaba Buhari ya zabi dawo da shi bayan ga su a cikin aiki har yanzu. Wadannan jami'ai, wasun su daga arewa, na ganin shugaba Buhari bai yi masu adalci ba tare da yin tambayar, "mu kenan ba zamu taba shugabantar hukumar ba?".

Jaridar Premium Times ta bayyana cewar wasu jami'an DSS sun shaida mata cewar hatta cire Seiyefa da Buhari ya yi, akwai hannun wasu na kusa da shi da basu ji dadin cire Daura da Osinbajo ya yi ba, musamman ganin yadda shi Seiyefa ya fara nuna masu alamun ba zai yi aiki bisa son rai ba. Premium Times ta ce, a wani binciki da ta gudanar, shugaba Buhari da kansa ya san yana fuskantar tarnaki daga jami'an tsaro a kudirinsa na yin tazarce. 

Manyan jami'an hukumar DSS sun shaidawa Premium Times din cewar ba zasu taba yafewa Buhari kuma sun gwammaci taimakawa jam'iyyar adawa a kan su taimaki Buhari ya kara cin zabe a 2019. 

No comments:
Write Comments