Saturday

Home HOTUNA : "Yan Sanda Sun Damke "yan Bangar Siyasa A Kano.
A yau Juma’a ne rundunar ta 'yan sanda reshen jihar Kano ta yi gabatarwa manema labarai wasu 'yan bangar siyasa wadanda aka kama a yayin zabubbukan fidda gwani na jam’iyyu daga Talata 2 zuwa Juma’a 5 ga watan Oktoban 2018.


 Cikin wadanda aka kama har da wani dan fashi da makami wanda an dade ana nemansa wato Bashir Musa da aka fi sani da Gachi wanda ke addabar Unguwannin Hotoro, Na'ibawa, Mariri da sauransu a birnin Kano. 


Kakakin rundunar yansandan jihar Kano, SP Magaji Musa Majia ya ce sun kama 'yan bangar siyasar da mugayen makamai masu yawa da suka hada da adda, barandami, sanduna da wukake. Yace dukkanin yandaban da ke hannun su zasu mika su zuwa kotu domin ayi musu hukunci dai dai da abinda suka aikata. 


Daga karshe SP Majia, ya tabbatar da cewa rundunarsu za ta cigaba da aiki ba dare ba rana wajen kame duk wasu 'yan bangar siyasa a Jihar Kano don ganin anyi zaben shekara ta 2019 cikin lafiya da kwanciyar hankali.

No comments:
Write Comments