Saturday

Home Ko Kunsan Da Naman Gawa Ake Abincin Zaman Makoki A Wata Kabila : Karanta
A koda yaushe mutanen bugisu suna zaune ne yankuna na duwatsu, guri wadanda akwai hasumiya na mount elgon wanda ke a yankin Mbale na kudancin uganda.

Source : leadershipayau

  Wannan waje yana da kyau matuka wajen noma a kasar, wanda ya sanya mutanen suka kasance kwararru sosai a wajen noma, mafi yawan wajen yakan kai taku 8,000 yayin da mafi karancin wajen yakan kai taku 4,000 saman matsayin teku, kusa ko kuma hade da tudun. Akwai kogo da kuma koguna kamarsu Manafawa, Sorokho da Lwakhakaha da kuma gandu inda mutan Imbalu ke wanke al’auransu a la’adance kafin zuwa tiyata, sukanje kogin da sassafe domin maida tsokarsu (muscle) kangararre (numb).

Yare Bagisu suna magana da yaren Lagisu ,wanda wasu lokutan ake wa lakabi da Lumasaba yare mallakin iyalan Niger- congo. Bagisu dake kusada babukusu na yammacin kenya suna da rinjaye na Lubukusu yaren babukusu sannan kuma bagisu dake tsakiyar bugisu suna mahana da yaren Lugisu Tarihi ya nuna cewa mutanen Bagisu sun rabe ne da bukusu wani lokaci wajejen karni na 19th.

Tattalin arziki Kamar sauran kabilar bantu,bagisu manomane wadanda wasunsu kanyi noman Arabica coffee,sukanyi noman auduga,kadan daga cikinsu kan noma taba(tobacco) Suna noma Ayaba wanda suke nomashi musamman domin abinci wanda haka baya hanasu saidashi domin samun wasu kudade,mutanen bagisu suna noman Masara, wake,dawa, sorghum, doya da kuma rogo, a yanayinda ya kasance noma baiyi albarka ba kuwa sukan sami dawa da sauran kayan abinci daga ltesots, banyoli, jopadhola, bagwere da kuma sabinys wanda suke amfani dashi wajen bikin kaciya na Imbilu.

Mutanen bagilu sukanyi kasuwanci da garuruwanda suke makobtaka dasu sannan kuma abubuwan da suke cinikayya dasu ya hadada,kayan abinci, sugar, gishiri, sabulu ,shanaye da kuma kayayyaki irin na kadae kade. Dawa da masara akan adanasu ne arumbu bayan sun bushe wanda ake dagashi sama da duwatsu domin kariya daga ruwa ko kwari masu cin hatsi, sukanyi mafarautar namun daji domin abinci kamar su Gada.

A lokuta irin na yaki maza suna amfani da kwari da baka wanda ke dauke da guba a bakin bakan,kowanne gidan sun kasance sun mallaki dabbobi kamar shanaye,domin madara,raguna ,awaki domin kasuwanci,akan ajiye kaji domin ci,amma lokacin bukukuea kadai. Tukwane irin na kasa yakasance abin kyauta a tsakanin mutanen bagisu,yayin da ake katange matan da suke dauke da juna biyu daga zuwa inda akeyin wadannan tukwane. Bayan anyi aure miji yakan baiwa matarsa kyautar fili na noma yayinda zai gyara ya kuma nome filin inda ita kuka matar zatayi shuka.idan kuwa amfani ya nuna mata da mazan sukan hadu domin girbe amfanin.

Babban ‘da’ yawanci shike gadon mahaifinsa,wannan bai zama tilas ba domin kuwa a wasu lokutan dangin mahaifi sukan hana yaro wannan gado,hakki ne akan kowane babban da ya kula da yan uwansu har zuwa lokacin aure,yayinda zaiyi amfani da kudin aure da ya samu na kannensa mata wajen yin nasa auren,da kuma auren yan uwansa maza tareda kayan mahaifinsa da ya gada,babban da zai iya mallake matayenda mahaifinsa ya bari ya maidasu matansa Addinin
Al’ummar bagisu sunyi imani bautar abin bautarsu mai suna Wele Lunya,wanda aka sani kuma da Wele Namangako weri Kubumba, a cewarsu Abin bautarsu (Allahnsu) na sanya fararen kaya domin bayyana yanayinsa na tsarki (holy nature) a cewarsu Allansu yanada mataimaka guda uku wanda suke kira da wele lunya ,mataimakan sun kasance kamar haka Wele maina- wanda keda alhakin kulawa da dukiyar da ta danganci dabbobi shine kuma yake sanya bakarrarriyar saniya(barren) ta haihu domin burge shi kuwa mutum yakan iya kai hadaya ta bakarrriyar saniya gareshi a kushewar wali(shrine) Wele nabende wanda keda alhaki akan dukiya ta bangaren hatsi da kuma nomar ayaba akan mishi hadaya ta hanyar barin tarin nunannun ayaba a filin noman ayabar ‘Welenkbulondele ahike’ da alhaki a kan haihuwa.

Maza sun kasance masu matukar taka tsantsan a wajen tafiya ko hawa wani abu yayinda mata keda dauke da juna biyu domin kuwa faduwa yakan iya janyo wa mace yin bari a cewarsu,bayan mace ta haihu za’a binne cibiya cikin taka tsanta a bayan gida,za’a zuba giya a wajen da akayi haihuwar sannan a shuka bishiyoyi guda biyu a kofar gida masu suna mbaga da mwima,bayan mace ta haihu zata dauki tsawon kwana goma sha biyar a katange gefe daya ita kadai bayan nan kuma zata aske gashin kanta tas.

Girki ya kasance abu mai matukar muhimmanci,matan da sukayi aure a kabilar bagisu akan ce sun tafi” Bufumbo college” ma’ana sun tafi girki,idan namiji yanaso ya kori matarsa kuwa, zai fara shiga kitchem da yin girkin abinda zai ci,namiji yayi girki babban abin kunya ne ace namiji yayi girki dan haka ma zai zama na cewar matarsa batada amfani.

Mutuwa Bayan mutum ya mutu, gawarsa za ta kasance a gidan har na tsawon kwana uku har zuwa lokacin da ‘yan uwan mamaci za su hallara, da almuru kuwa za a dauki gawar shi mamacin a jefar a bola mafi kusa yayin da da daddare za a yi ta busa kaho. Sai kuma a fada wa yara cewa namun jeji suna tafe domin cinye wannan gawar. Cikin dare kuwa matayen da suka kasance makusanta da wannan mamaci za su koma inda aka yarda gawan su yanko wasu bangarori na jikin mamacin domin amfani wajen makoki, akan yi zaman makoki na kwana uku a gida inda a wannan lokacin zai kasance ana cin naman wannan mamaci da aka yanko. Wannan ne al’adar kabilar. Masu iya magana kan ce “dai-dai din wani, karkataccen wani”. Allah daya gari bamban.


Read More at: leadershipayau.com
No comments:
Write Comments