Thursday

Home › › Kungiyar Matasan APC na Shirin Juyawa Buhari Baya.




Labarin da mu ke samu yanzu shi ne cewa wata Kungiyar Matasa da ke tare da Jam’iyar APC mai mulki mai suna APC National Youth Vanguard na tunanin janye mubaya’ar ta ga Gwamnatin Shugaba Buhari. Kungiyar APC National Youth Vanguard za ta bar goyon bayan Buhari Source: Twitter 


Jiya ne APC National Youth Vanguard ta sanar da cewa akwai yiwuwar ta janye goyon bayan da ta ke ba Gwamnatin nan ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Jam’iyyar APC da ke karkashin Kwamared Adams Oshiomole. Kungiyar Matasan wanda da ita aka yi ta gwagwarmaya a zaben 2015 ta nuna cewa fadi-tashin da tayi sam bai yi mata rana ba. Shugaban APC NYV ESV Jibrilla Madu Gadzama yake cewa Gwamnatin nan ta Buhari tayi watsi da su gaba daya. 



Bisa dukkan alamu dai Kungiyar ta manyan matasa Masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhariwanda ke tare da Jam’iyyar APC ta na tunanin komawa wajen Atiku wanda ya lashe tikicin takarar Shugaban kasa a PDP a makon da ya wuce. 



A jawabin da Kungiyar ta fitar, wanda ya zo hannun NAIJ Hausa, Shugaban APC NYF ya nuna takaicin sa na cewa sun yi kokarin ganawa da Gwamnati amma an ki ba su dama. APC NYF dai tana cikin Kungiyoyi 187 da APC ta san da zaman su. Dazu kun ji cewa Jam'iyyar APC mai mulki ta maidawa INEC martani na cewa ba ayi zaben fitar da 'Dan takara a Zamfara ba. Shugaban APC na kasa Kwamared Adams Oshiomole yace ba haka abin yake ba. 
No comments:
Write Comments