Tuesday

Home › › Mutane 5 Sun Mutu Sakamakon Harin Da Yanbindiga Suka Kaiwa Wasu Matafiya A Adamawa
.
Mutane 5 Sun Mutu Sakamakon Harin Da Yanbindiga Suka Kaiwa Wasu Matafiya A Adamawa.


An kashe mutane 5 a harin da yan bindiga suka kai wa matafiya a Adamawa – Yan sanda  Yan sanda a ranar Talata, 16 ga watan Oktoba ta tabbatar da kisan mutane biyar a wani hari da yan bindiga suka ki akan matafiya a kauyen Bali dake katamar hukumar Damsa na jihar Adamawa. Wasu mutane hudu kuma sun yi nasarar tserewa da raunuka inda suke kwance a asibiti, inji ýan sandan. 

Kakakin ýan sanda a jihar, Othman Abubakar yace matafiyan na a hanyarsu na zuwa Jalingo amma sai ýan bindigan suka far masu a hanyar Numan-Kpasham a daren ranar Litinin.

 An kashe mutane 5 a harin da yan bindiga suka kai wa matafiya a Adamawa – Yan sanda

 Source: Depositphotos 

Mista Abubakar yayi kira ga mutane dasu kwantar da hankalinsu cewa ýan sanda sun fara bincike a cikin lamarin.
No comments:
Write Comments