Wednesday

Home labarin Yadda na sulale na bar Nigeria : Nnamdi Kanu
Shugaban kungiyar ‘Indigenous People of Biafra (IPOB)’, Nnamdi Kanu, ya yi bayani a kan yadda ya sulale daga Nijeriya a lokacin da sojoji suka rutsa da shi a gidansa.
 Mista Kanu, ya bayyana wannnan lamarin ne a hirarsa da wata tashar talabishan na kasar Isra’ila ya kuma watsa ta kafar sadarwa na zamani ta YouTube a ranar Litinin, ya ce, ‘yan uwansa ne suka taimaka masa har ya fice daga cikin kasar nan.


 “Sojojin Nijeriya sun bini gida ne don su kashe ni kai tsaye,” a cewar Mista Kanu, sojojin sun zo gidansa ne dake jihar Abiya don su kawar dashi, kafin ya bace. “Sun kashe mutum 28 a wannna kokarin,”
 inji shi.
 “Mutane na suka fitar dani kafin su same ni suka kuma fitar dani zuwa wajen kasar. Ina matukar murnar tsira zua wurin da nake jin ina cikin aminci fiye da dukkan ko ina a fadin duniyar nan.”

 Mista Kanu, wanda kuma yana da shaidar dan kasa a Birtaniya, ya ce, ya na matukar sha’awar zuwa kasa birtaniya amma ba shi da aminci da kasancewa a can. Dan tawayen, wanda ya tsere bayan karya sharddodin belin da aka bashi ya yi ikirarin cewa, a kwai ‘yan kabilar Ibo miliyoyi yahudawa wadanda ya kamata kasar Isra’ila ta tabbatar da ta kare su.

 “Dole Isra’ila ta tsaya don kare akidar yahudanci da yahudawa a dukk inda suke a fadin duniyar nan,” 
 “A na ci gaba da ci mana mutumci, mutanenmu na ci gaba fuskantar wahala, na kuma yi imanin cewa, hakkin Isra’ila ne ta tabbatar da cewa, kasar biyafara ta samu ‘yancin kanta a matsayin ‘yantacciyar kasa a Afrika.” 

“Biafra na da al’umma fiye da Miliyan 70 a fadin duniyar nan. Ana kiranmu yahudawan Afrika da ke warwatse. Wadanda suka danganta kansu da tsatson yahudanci sun kai mutum Miliyan 50,” inji shi.

Da aka tambaye shi yadda wadannan Miliyoyin yahudawa ‘yan Nijeriya da ya ce suna nan yadda suke gudanar da ayyukan bautarsu, Mista Kanu ya ce, suna yin addu’arsu ne ta hanyar karanta littafin Attaura.”

“A kwai ‘yan Nijeriya da yawa da suke bautar yahudanci kamar yadda ,muke yi a kungiyar IPOB. A lokacin da adinin Kirista ya iso kasar nan tare da ‘yan mulkin mallaka ne aka danne addinin yahudanci, muna son komawa baya yadda lamarin yake kafin zuwan ‘yan mulkin mallakar.


Ya wancin matsalolin da muka fuskanta Turawa suka kawo mana su.


“Muna son kasar Yahudawa mai cikakken ‘yanci, Biafra da keda cikkaiyar ‘yanci daga duk wani abu daga Nijeriya, a saboda wannna dalilin ne mu keda ‘;yanci
 tun kafin ma Turawa su shigo kasar nan, ana kuma muna kamar tsoro cewa in har Biafra ta yi kusa kusa da Isra’ila, wai mutum Miliyan 70 za su niki gari zuwa kasar Isra’la, lallai wannan bahaka bane.”
“A lokacin danza dawo Nijeriya a shekarar 2015, an kama ni aka kuma gufarabar da ni a gaba kotu, koytu ta kuma sake har sau 3, muna neman a bamu kasar Biafra, lalai a bamu kasar Biafra.” An kama shi ne tare da wasu mutum 3 a ranar 14 ga watan Oktoba na shekarar 2015 a garin Legas, daga nan ne mai shari’ar Binta Nyako ta bayar das hi a kan beli a anranar 25 ga watan Afrilu a bisa dalilin rashin lafiya aka kuma daga shari’a zuwa wayan Nuwamba.


Read More at: Leadershipayau.com
No comments:
Write Comments