Monday

Home 2019: Sabon rikici ya barke a jam'iyyar PDP ta jihar Plateau kan zaban mataimakin Useni
Wannan na zuwa ne mako guda bayan jam'iyyar tayi taron shugabanin ta a garin Jos inda suka yanke matakin goyon bayan Mr James Dalok a matsayin mataimakin dan takarar gwamnan jihar, Jeremiah Useni.
Sakon bayan taro da jam'iyyar ta fitar ya yi kira ga 'ya'yan jam'iyyar su yafe wa juna saboda cigaba jihar.
SOURCE HAUSALEGIT.NG

Sai duk da hakan, an gano cewa wasu jiga-jigai a jam'iyyar ba su gamsu da hanyoyin da aka bi wajen zaben Dalok ba wanda hakan ya sa suka shigar da kara a hedkwatan jam'iyyar da ke Abuja inda suke bukatan a maye gurbin Dalok.

Majiyar Legit.ng Hausa ta gano cewar wadanda suka shigar da karar zuna zargin Ciyaman din jam'iyyar na jihar, Damishi Sango da yin magudi wajen zaben tare da cewar tsohon Ministan Wasannin bai tuntubi masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Mangu ba inda aka zabo mataimakin gwamnan.

An gano cewar wani tsohon sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Shedrack Best da wasu mutane hudu ne aka fara zaba domin takarar mataimakin gwamnan amma daga baya akayi watsi da su aka zabi Dalok hakan yasa suka shigar da kara a Abuja.

Farfesa Best ya tabbatar da afkuwar wannan lamarin yayin da ya yi magana da Punch a ranar Lahadi a garin Jos.

Ya ce,
"Gaskiya ne munyi kara a hedkwatan jam'iyyar mu saboda ba mu gamsu da yadda aka zabi mataimakin gwamna ba. Ba za mu iya warware matsalar da kan mu ba shi yasa muke kokarin janyo hankalin shugabanin jam'iyyar.
"Muna tunanin bai dace wasu su saba doka ba kuma a saka idanu ba tare da naukan mataki ba. Muna ganin ya dace a kare jam'iyyar. Muna ganin an yaudare mu yayin gudanar da zaben mataimakin gwamnan."

Sai dai Sakataren yadda labarai na jam'iyyar na jiha, John Akans ya ce jam'iyyar ba ta damu da karar da aka shigar ba.

Ya ce,
"Batun nada mataimakin gwamna ba zabe bane. Dan takarar gwamnan yana da ikon ya zabi abokin takararsa muddin ya tuntubi jam'iyya kuma hakan aka yi."
No comments:
Write Comments