Tuesday

Home A Yanzu Dai Bazamu Iya Biyawa ASUU Bukatunta Ba : Cewar Gwamnatin Tarayya.
A ranar litinin, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a yanzu ba ta da isassun kudaden da za ta iya amfani da su wajen biyan bukatun kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU. Ministan ilimi, Adamu Adamu ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Abuja, yana mai alakanta gazawar daga faduwar tattalin arzikin kasashen duniya, ciki kuwa har da Nigeria.
Gwamnatin tarayyar, ta kuma zargi gwamnatin da ta shude, karkashin marigayi Umaru Musa 'Yar Adua, akan daukar wannan babban alkawari ga kungiyar ta ASUU, duk da kasancewar akwai makudan kudade da kasar ta samu daga safarar mai. "Bari na fara yi maku matashiya, wannan lamari na shigarsu yajin aiki, ya samo asali ne tun a 2009, a lokacin gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar Adua, a lokacin ne aka sa hannu kan yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU, na daukar nauyin jami'o'in gwamnatin tarayya da ke fadin kasar," a cewar sa. A cewar ministan ilimnin, an ware kudade da suka kai N1.3tr don daukar nauyin jami'o'in gwamnatin tarayya na kasar, har tsawon shekaru 6. Sai dai a lokacin kasar na samun makudan kudade daga safarar mai. A lokacin tabbas ana sa ran gwamnati za ta iya cika wannan bukatu na kungiyar ASUU, tunda akwai kudi a kasar.
"To sai, biyo bayan faduwar darajar danyen mai a kasashen duniya a shekarun baya, sai Nigeria ta shiga cikin matsatsin tattalin arziki. Tun bayan hawan wannan gwamnati, tattalin arzikin ya ci gaba da tabarbarewa, wanda ya shafi kowanne fanni na kasar, ciki kuwa har da fannin ilimi,"
a cewarsa. Sai dai Mr. Adamu ya bayyana cewa a yanzu kasar ta fara farfadowa daga durkushewar tattalin arziki, kuma farashin mai ya fara haurawa, "wanda idan hakan ya ci gaba da tafiya, to za a bunkasa fannin ilimi, wannan ne ya kamata ASUU ta fahimta, da ma duk wani dan Nigeria". Ministan ya kuma roki ASUU, iyaye da kuma dalibai da su kara hakuri a kan yadda fannin ilimin kasar ke tafiya yanzu. SOURCE@LEGITHAUSA.NG
No comments:
Write Comments