Friday

Home Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Dr. Leo Igwe, shugaban Mulhidan Najeriya.
Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Dr. Leo Igwe, shugaban Mulhidan Najeriya Tunda ya hau mulki a shekara ta 2015 bai boye tsanar da yakewa yan Shi'a ba, gwamnatin sa tana daukar su tamkar wasu masu laifi wadanda basu da 'yanci.


 An dakatar dasu dagayin tattaki daga Kaduna zuwa Abuja don neman yancin su,jami'an tsaro suna kashe su a fadin kasar nan. Sannan a kama shugaban su Ibrahim Elzakzakiy tsayin wasu shekaru an hana a sakeshi .

Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Leo Igwe Wannan yanki ne na bayanai da ja-gaban marasa addini na Najeriya, watau Nigeria Humanists Association, kan jawo hankalin gwamnati ta daina kashe 'yan shia: Ya kamata shugaban kasa Muhammad Buhari ya kawo karshen zubda jinin yan Shi'a da akeyi a fadin kasar nan.

Duk wani dan Shi'a da aka kama da laifi a gurfanar dashi a gaban kotu bawai a harbeshi akan titi ba ,ya kamata a girmama bukatun su. Shi'a yan Nageriya ne ya zama dole a mutuntasu kuma a basu girman su.

 Read more:Legithausa.


No comments:
Write Comments