Saturday

Home "Bantaba Karbar Albashi Ba Tunda NA Hau Kujerar Gwamna" : Cewar Gwamnan Apc
Wata Sabuwa "Bantaba Karbar Albashi Ba Tunda NA Hau Kujerar Gwamna" : Cewar Gwamnan Apc


A hirar da akayi da shi a wani shiri mai suna
'Ogeni Till Day Break' a ranar Asabar a Osogbo,
gwamnan ya ce babu bukatar ya karba albashi
saboda jihar dauke masa dukkan hidindimun
rayuwa kamar muhalli, abinci, man da zai saka
a mota da sauransu.

Gwamnan har ila yau ya kara da cewa ba shi da
wata asusun bankin ajiya kamar yadda kamfanindillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

" Ban taba karbar albashi ba tunda na zama gwamna a jiha ta. Jihar ke ciyar da ni, ta saka min man fetur a mota ta kuma samar min da muhalli. Idan an dauke min dukkan wadannan, bana bukatar kudi.

"Ba ni da asusun ajiyar banki a ko ina. Ba ni da gida ila wadda na gina kafin in zama gwamna. Duk mai so yana iya zuwa ya yi bincike idan ina da asusun ajiya a banki. "
inji Aregbesola.

An sa ran Aregbesola zai mika mulki ga
zababben gwamna, Gboyega Oyetola a ranar 27
ga watan Nuwamban 2018 amma ya ce zai fice
daga gidan gwamnati a ranar 19 ga watan
Nuwamba saboda ya bawa sabon gwamnan
damar yin gyare-gyare.

Aregbesola ya bayyana cewa yana son ya koma
gefe guda ya huta domin ya dade yana siyasa tun lokacin da ya ke makarantar sakandire.
No comments:
Write Comments