Wednesday

Home Rashin Imani ruwa ruwa: Matsafa sun kwakule idanun wani karamin yaro a Nasarawa
Majiyar Legit.com ta ruwaito mahaifin yaron mai suna Agadi Ajeh mai shekaru 47 yana bayyana yadda tsautsayi yah au kan yaronsa Monday, inda yace da lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, yayin daya kwance da iyalinsa da misalin karfe 1 na dare.

Agadi yace yana kwance sai yaji yaronsa yana ihu yana neman taimako, fitarsa keda wuya sai ya fahimci an yi garkuwa da dansa ne, nan da nan suka tashi gungun matasa don nemo yaron, bayan wani dan lokaci suka gano shi kwance jina jina an kwakule masa ido.


Mahaifin yaron yace “A lokacin da muka isa inda yaron yake, mun tarar da shi an rufe masa fuska, an daure masa kafafu da hannuwa, an kwakule masa idanu ga jini ya malaleshi gaba daya, mutuwa kawai yake jira.

“Wanene wannan ya aikata ma yarona haka? Sun sace shi daga gidana da tsakar dare yayin da nake barci, suka kai shi wani waje mai nisan kilomita biyu daga gidana.” Inji Adagi, mahaifin yaron.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Nassarawa, ASP Samaila Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, har ma yayi karin haske inda yace cewa Monday ya fara kai kara ga iyayensa cewa ya fahimci kamar wasu mutane na neman sace shi su cire masa ido, amma iyayensa suka yi biris da shi.

“Koda yaron ya fada musu matsalar dake damunsa, iyayensa basu dauki mataki ba, kuma basu kai ma Yansanda kara ba, sai suka yi biris da shi, sai gashi bayan watanni da wannan gargadi da yaron yayi musu an sace shi, kuma an cire masa idanu.” Inji shi.

Sai dai ASP Usman yace kwamishinan Yansandan jahar ya aika da jami’an Yansanda zuwa inda lamarin ya faru don tabbatar da sun kama duk masu hannu cikin wannan ta’asa, tare da gurfanar dasu gaban kotu, amma a yanzu Mondaya na samun kulawa a asibitin Dalhatu Araf.
No comments:
Write Comments