Tuesday

Home Rikicin APC: An bawa Oshiomole cin hancin $500,000 amman Ya 'ki Karba
Gwamnan ya bukaci shugaban APC ya baiwa na
kusa da shi tikitin takarar zaben gwamna. AmmaOshiomole ya jaddada cewa ka’idojon jam’iyyar za’a bi. Kana, uwar jam’iyyar APC ta yi kokarin sulhu da gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, amma gwamnan ya kiya, ya lashi takobin cewa shi zai fitar da dukkan yan takara.

Apc Chairman

Majiyar Sahara Reporters ta bayyana cewa
sabanin zarge-zargen da ake yiwa Oshiomole
cewa ya karbi cin hanci daga hannun wasu
jigogin jam’iyyar, wasu yan takaran ke kokarin yi
mas tuggu.

Wata majiya mai karfi da aka sakaye sunanta
tace:
“Abin ya kai, wani gwamna ya baiwa Oshiomole , kimanin $500,000 domin samun tikitin gwamnan jiharsa.” Daya daga cikin yaran gwamnan ya kawo kudaden ofishi Oshiomole amma bai amsa ba.”

“Kawai sai shugaban APC ya sanar da kwamitin gudanarwar jam’iyyar kan abinda ya faru kuma ya sanar da wasu shugabannin jam’iyyar.”


Mun kawo muku rahoton cewa Kan gwamnonin
yankin Yarbawa shida ya rabu kan shugaban
jam’iyyar All Progressives Congress, Adams
Oshimohole, Legit Hausa ta samu rahoto.
Jaridar Punch ta bada rahoton cewa yayinda
wasu na kokarin ganin cewa an cire Oshiomole
daga kujerarsa bisa ga rikicin da ya kawo
jam’iyyar, wasu sun ce babu yadda za’ayi a
ciresa.

Wadanda suka yi mubaya’a ga Oshiomole sune
gwamnonin da ke biyayya ga babban jigon
jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda
ya kunshi gwamnan jihar Legas, Akinwumi
Ambode; gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola;
gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

Gwamnonin suke yiwa Oshiomole tawaye sune
gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun da
gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu.
Sun kulla gaba da Oshiomole ne sanadiyar
abinda ya musu a zaben fidda gwanin jam’iyyar
a jihohinsu.

SOURCE : HAUSALEGIT.NG
No comments:
Write Comments