Saturday

Home Wasikar Ty Burutai Zuwa Ga Dakaru Soji Masu Yaki Da Boko Haram.
Kadan daga cikin wasikar da TY Buratai ya aikawa dakarun sojin na cewa:

1. Ina so nayi amfani da wannan damar, don tunatar da ku irin karfafa guiwar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yi, wajen samar da kayan aiki da kuma kyakkyawan muhalli don gudanar da wannan aiki naku, kamar dai yadda ya bayyana a jawabin da ya gabatar a ranar da aka kaddamar da gidauniyar tunawa da dakarun sojin kasar. A karon farko: Buratai ya rubuta wasika ga dakarun sojin da ke yakar Boko Haram
TY-BURUTAI

 2. Hakika ba a san rundunar sojin Nigeria da lalaci ko munanan dabi'u ba. Mun dakile manyan hare hare da kuma dakile tashin hankula da ke addabar kasar a cikin shekaru 3, a yanzu haka muna ci gaba da wannan kokarin. Haka zalika, duk jami'in sojin da aka kama ya juya baya ga bautawa kasarsa to kuwa zai fuskanci hukunci a kotun ladabtar da jami'an soji. Kamar yadda kuka sani, hukuncin zai iya zama mai tsanani.

 3. A matsayina na Hafsan rundunar sojin kasar, ina iya bakin kokarina na tabbatar da walwalarku.

A domin haka ne, na bayar da umurni a biyaku alawu alawus dinku akan lokaci. Haka zalika, na bayar da umurni da cewar a rinka tura dakaru a rukuni rukuni. Kamar yadda aka soja a fagen daga, ina sane da illolin da yaki ke jawowa. Domin hakan, na bayar da umurni na baiwa jami'an da ke son ganin ilansu damar yin hakan.

4. A kokarinsu na fadada ta'addancinsu, 'yan ta'addan Boko Haram sun dawo da yin wa'azin karairayi da hurewa jama'ar shiyyar Kudu-maso-kudu kunne don bin wannan hanya tasu. Don dakile hakan, na bayar da umurni ga wasu sashe sashe na harkokin soji da kuma bangaren Limaman coci dana masallatai, da su dukufa wajen wayar da kan jama'a dangane da illolin ayyukan mayakan na Boko Haram. Haka zalika, na kafa wata runduna ta jami'an soji akan kafofin watsa labarai na yanar gizo, don dakile yaduwar ta'addanci a yanar gizo da kuma baiwa rundunar damar kula da daukar ma'aikata a kafar. Don haka, kada ku bari ku fada cikin komar karairayin da 'yan ta'addan ke yadawa. Dole ne mu jajurce wajen yakarsu, cikin dadi da rashinsa.

5. A wannan gabar, bari na godewa al'ummar Nigeria bisa namijin kokarinsu wajen goyon bayan rundunar soji, musamman a bangarorin addu'o;i da kuma karfafa guiwa, hadi da fatan alkairi. Hakika rundunar soji an samar da ita domin ku.

Zan yi amfani da damar wajen yin gaduwa gareku, dakarun dojinmu, bisa namijin kokarinku a lokutan dare da rana, bazara da damina, sanyi ko zafi, don kare kasarmu. Himmatuwarku da kuma kwazon da kuke nunawa wajen sadaukar da rayukanku hakika abun a yaba ne kuma a baku lambar yabo akai.

 Allah ya albarkaci kasarmu Nigeria.


Source : Dailytrust
No comments:
Write Comments