Tuesday

Home Yadda gwamnan PDP ya jagorancin korar 'yan APC daga majalisar jiharsa.
'Yan majalisar na APC sun shiga zauran majalisar a safiyar yau inda su kayi wata zama cikin gaggawa kuma suka dakatar da wasu 'yan majalisar guda 11.

Nse Ntuen mai wakiltan mazabar Essien Udim a jihar na ya jagoranci zaman.

Sauran yan majalisar hudu sune, Gabriel Toby mai wakiltar mazabar Etim Ekpo/Ika; Otobong Ndem mai wakiltar Mkpat Enin; Victor Udofia mai wakiltar mazabar Ikon sai Idongesit Ituen mai wakilatan mazabar Itu.

Suna nan a cikin harabara majalisar a yayinda gwamnan jihar Udom Emmanuel wadda ke jam'iyyar PDP ya iso majalisar tare da jami'an tsaro da wasu matasa masu goyon bayan PDP kuma ya tarwatsa zaman da 'yan majalisar keyi.
An yi harbe harbe da kana an kone mota guda a hayaniyar da ta faru a majalisar a yau.

A baya. Legit.ng ta kawo muku cewa yan sanda sun sake rufe majalisar dokokin na jihar Akwa Ibom karo na biyu a cikin mako biyu.
An gano cewa yan majalisar jihar biyar da aka sallama kwana-kwanan nan ne suka kai hari majalisar tare da jami'an 'yan sanda da 'yan daba.
Rahoton ya bayyana cewa 'yan majalisar da aka sallama na dauke da sandar ikon majalisar kuma sun shirya tsige kakakin majalisar kana su dakatar da mambobi 21 na majalisar da kuma tsige gwamnan jihar.

Wannan na zuwa ne wasu 'yan kwanaki bayan shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya umurci yan sandan su bar harabar majalisar domin ya majalisar su shiga zaurensu su cigaba da ayyukansu.

SOURCE @LEGIT.NG
No comments:
Write Comments