Thursday

Home Yau alhamis Shaidu Sun Tabbatar Da Yadda Maryam Sanda Ta Kashe Mijinta Bilyaminu.
A yau Alhamis ne shedu uku suka bayyana wa kotu yadda aka yi Bilyaminu Bello da ake zargin matarsa, Maryam Sanda da kashe shi ya mutu.
Bello, dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP na
kasa, Haliru Bello ya rasu ne a Nuwamban 2017.

An tuhumar matarsa Maryam Sanda, mahaifiyarta, Maimuna Aliyu; dan uwanta, Aliyu Sanda da mai aikin gidansu, Sadiya Aminu da hannu cikin kisarsa.

A yau Alhamisa ne lauya mai shigar da kara,
Fedelis Ogbebe ya gabatarwa kotu shedu uku,
Hamza Abdullahi (mai wanki da guga), Simon
Okon da Usman Aliyu domin su bayyana kotu
abinda suka sani a kan rasuwar Bilyaminu.

SOURCE AT LEGITHAUSA.NG

Shari'ar Maryam Sanda: Shedu sun fadawa kotu yadda aka kashe Bilyaminu.

Ga abinda Mr Abdullahi mai wanki da guga a
gidan ya fadi:
"A ranar 17 ga watan Nuwamban 2017 misalin karfe 1-2 na dare ina kwance sai na ji ihun Bilyaminu, na tashi na nufi idan ya ke sai na samu ya rufe bangaren kirjinsa da riga,bayan mintuna biyu sai matarsa ta fito rike da makulin mota ta bukaci mu taimake ta saka Bilyaminu cikin mota.
"Da mu kayi kokarin daga shi sai muka ka jini. Ni da wasu mutane biyu muka saka shi cikin mota yayin da matarsa ta tuka motar. Da muke cikin motar ta tambayi ni Asibiti mafi kusa sai na fada mata Maitama Clinic.
"Da isar mu asibitin mun hada da nurse ta da kira mana likita. Likitan ya tambayi Maryam abinda ya faru har sau uku amma ba ta amsa ba. Hakan yasa likitan ya ce mu tafi dashi wani asibiti, daga nan muka tafi Maitama GeneralHospital nan ma likita ya tambaya abinda ya faru.
"Daga nan ne Maryam ta fada wa likitan cewa suna ta fada ne da mijinta tunda safe. Likitan ya duba Bilyaminu sai ya gano cewar ya mutu.
 Likitan ya bukaci ta kira 'yan uwansu a waya amma ta ce masa wayanta da na mijinta sun lalace wajen fada. Ya bata wayansa ta kira yan uwanta ta fada musu abinda ya faru.
"Yan uwanta sun taho daga baya suka karbi gyalenta suka rufe gawar Bilyaminu. Daga nan mahaifiyar Bilyaminu ta iso ta bude fuskan dan ta inda ta lura akwai alamar yankan wuka a kirjinsa da cizo a kirjinsa da kunnensa. Akwaiyanka a yatsansa da kuma al'auransa.
"Da komawarmu gida sai na lura cewa an goge jinin da muka bari kafin zuwa asibiti, na tambayi Alabi ko shine ya goge jinin amma ya ce ba shi bane."7

Mr Okon ASP na yan sanda shima ya bayar da
nasa labarin abinda ya sani. Kazalika Mr Aliyu,
abokin Bilyaminu shima ya fadawa kotu abinda
ya sani game da rasuwar.
Bayan sauraron dukkan shaidun, alkalin kotun
mai shari'ah Yusuf Halilu ya dage cigaba da
sauraron shari'ar zuwa ranar 26 ga watan
Nuwamba.
No comments:
Write Comments