Saturday

Home An janye magungunan hawan jini daga kasuwa da farmasis, an gano suna sanya cutar kansa
Wani bincike da Teva Pharmaceuticals ta fitar ya bayyana cewa akwai wasu magungunan hawan jini guda Biyu da shansu yana iya janyo kamuwa da ciwon cancer.


A wani bayani da Teva ta turawa FDA tace hada wadannan magunguna biyu masu suna Amlodipine da kuma valsartan yanada matukar illa.

Magungunan suna dauke da wani sinadari mai suna N-nitroso-diethylamine(NDEA) wanda wannan sinadari yana iya janyo kamuwa da cutar Kansa.

Duk wani mara lafiya da yake shan daya daga cikin wadannan magungunan biyu to ya gaggauta ziyartatar likitansa don neman shawara da bincike.

Sannan dakatar da shan maganin ba tare da wani bincike ba ka iya jefa mara lafiyar cikin hatsari.cewar Teva.
No comments:
Write Comments