Wednesday

Home Majalisar dattijai za ta canja sunan filin jirgin sama na Kaduna don karrama Abba Kyari
Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta raya sunan maraigayin janar din ta hanyar sanya sunansa a wani ginin gwamnati domin karrama shi.
Marigayi Abba Kyari dai shine gwamnan tsohuwar Jihar Arewa ta tsakiya kuma ya rasu ne a ranar 25 ga watan Nuwamba a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 80 a duniya.

Yan majalisar sun gabatar da wannan bukatar ne bayan wasu daga cikinsu sunyi ta'aziyya tare da jinjina ga marigayin janar din.
Sanatocin sun bayyana cewa mutuwarsa babban rashi ne ga kasa baki daya amma sun yiwa Allah godiya bisa rayuwa nagari da ya yi.
Majalisar ta ce za ta tura tawaga na musamman domin zuwa gidan marigayin domin yiwa iyalensa da al'ummar jihar Borno ta'aziyya.
Sanata Sabi Abdullahi na jam'iyyar APC mai wakiltan Niger ta Arewa ne ya gabatar da kudirin neman sauya sunan filin tashin jiragen Kaduna da na marigayin sannan Sanata Shehu Sani daga mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya goyi bayan kudirin.
Anyi kuri'a a kan kudirin kuma ya samu amincewar 'yan majalisar.
No comments:
Write Comments