Tuesday

Home Mata 3 daga cikin 15 da Boko Haram ta sace sun tsere.

Kungiyar Urgence Diffa, wacce ta tabbatar da kubutar matan uku daga hannun Boko Haram, ta kuma tabbatar da cewa a ranar Talata ne ake sa ran mahukuntan yankin na Diffa za su mika matan 3 a hannun iyalansu.

Da rabon shan ruwa gaba: Mata 3 daga cikin 15 da Boko Haram ta sace sun tsere

Da rabon shan ruwa gaba: Mata 3 daga cikin 15 da Boko Haram ta sace sun tsere

A daren ranar 24 ga watan Nuwamba ne 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka kai wani harin ba zata tare da sace 'yan mata 9 a garin Blaharde da kuma wasu 6 a garin Bandé da ke kusa da Toumour.

Haka zalika, Legit.ng ta tattara bayani kan cewa akwai wasu mata da kananan yara sama da 30 da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace a garin Ngalewa a jihar Diffa, gabanin sace 'yan matan 9.

No comments:
Write Comments