Monday

Home To fa ! : Wasikar obasanjo zuwa ga trumph na Amurka.
Tsohon shugaban mulkin nigeria olushegun obasanjo ya aike sakon ta'aziyyar sa zuwaga shugaban kasar amurka donal trumph, bisa rrasuwar tsohon shugaban na amurka george h. bush.


 mataimaki na musamman a bangaren yada labarai ga shi obasanjo  ya bayyanawa manema labarai cewar obasanjo ya samu labarin rasuwar george bush ranar jumua sannan labarin mutuwar ya girgizashi matuka.

"tsohon shugaban amurka george bush ya kawo sauyi ta fuskar canja alkiblar alaka dake kasashen africa da kasar amurka.
Wanna mutuwa bawai akwai ta shafi iyalai da yan uwan bush kawai ba , wanna mutuwa ta bush ta shafi duniya baki daya" cewar obasanjo

ya kara da cewar "ya kawo manyan nasarori ta fuskar kyautata alaka da duk kasashen duniya, dorewar demokaradiyya, kulla kasuwanci tsakanin kasashen africa da kasar amurka,wadannan abubuwa zasu cigaba da tuna mana da shi" cawar obasanjo acikin wasikar ta sa.

sannan obasanjo yace " george bush masoyin nigeria ne duba da yadda mulkinsa yayi silar samu kyakkyawar alaka tsakanin Nigeria da Amurka, Mna taya amurka alhinin rashin jarumin dattijo, masanin makamar aiki" ceawar obasanjo acikin wasikar ta sa.

obasanjo yace rayuwar bush abin koyi ce ga duk wadanda suke son kawo canji ta hanyar bautawa kasa.


No comments:
Write Comments