Monday

Home Yadda wani magidanci ya rasa hannunsa guda 1 a hannun dan uwansa da matarsa.
Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun ya bada izinin daure ma’auratanne biyo bayan gurfanar dasu da aka yi a gabansa kan zarginsu da tafka babban laifi, inda suka baiwa juna gudunmuwa suka guntule ma dan uwan mijin hannu da adda. 

 Sufeta Alhassan Jibrin ya shaida ma kotu cewa a ranar 21 ga watan Nuwamba aka kawo masa wannan kes a ofishinsa dake babban ofishin yansandan binciken manyan lauifuka daga ofishin DPO dake Okuta domin ya gudanar da binciken sirri. 

Dansanda Jibrin yace rahoton da suka samu shine cewa ma’auratan mazauna unguwar Koro Fulani cikin yankin Bankubu a karamar hukumar Okuta ta jahar Kwara sun kai ma wani dan uwan mijin matar mai suna Muntari hari.

 A wannan harin da suka kai masa kuwa, mijin matar, Malam Abubakar yayi amfani da adda wajen sassaran ma Munatari hannunsa na hagu, a dalilin haka ya guntule masa hannu, jini ya yi ta kwarara, laifin da Dansanda yace ya saba ma sashi na 97 da 243 na kundin hukunta laifuka. 

Sai dai ma’auratan sun musanta wannan tuhuma, inda uwargida Yar-Mallam Shagari ta bayyana ma kotu cewa Muntari ne ya fara neman rigimar mijinta, a cewarta shien ya fara kai ma mijin nata hari, kum duk kokarin da aka yin a rabashi daga mijin nata ya ci tura. 

Bayan sauraron bangarorin biyu ne sai Alkali Ibijoke Olawoyin ta bada belin ma’auratan akan kudi naira dubu goma kacal, da kuma mutane biyu da zasu tsaya musu akan dubu goma goma kowannensu, amma suka gaza cika sharuddan belin. Da wannan Alkali Ibijoke ta bada umarnin a garkamesu a gidan yarin gwamnatin tarayya dake Ilorin, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Disamba.
No comments:
Write Comments