Wednesday

Home Jigo a jam'iyyar APC ya fadi su waye ke tsoron tazarcen Buhari : Read more
Buhari ya zarceAliyu Idris Ibrahim, Shugaban karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna ya ce balagurbin 'yan Najeriya ne kadai ba su son Shugaba Muhmmadu Buhari ya yi nasara a babban zaben da ke tafe a watan Fabrairu. Shugaban karamar hukumar ya furta hakan ne a yayin da ya ke mika takardan kwangilan wasu ayyuka da aka bayar da mazabar Limancin Kona da ke karamar hukumar Zaria a jihar ta Kaduna. 
Gurbatattun 'yan Najeriya ne ke tsoron Buhari ya zarce Source: Depositphotos.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa shugaban karamar hukumar ya nada shugabanin unguwanni a kowane mazaba domin su saka idanu a kan 'yan kwangilar domin tabbatar da cewa ba ayi amaja ba.
Mr Idris-Ibrahim yace:
"Bana tantamar cewa shugaban kas Buhari ne zai yi nasara a zabe mai zuwa, kawai balagurbin 'yan Najeriya ne ke fargaban nasarar sa. "Buhari shugaba ne da ke na niyyar kawo canji na alheri a Najeriya, saboda haka ya kamata mu bashi kuri'un da zai taimaka masa ya kawo irin gyarar da ya ke son yi a kasar. "Mu kuma tabbatar mun bawa Gwamna Nasiru El-Rufai kuri'u da sauran 'yan takarar jam'iyyar All Progressive Congress, APC, da ke takarar zabe a dukkan matakai." Shugaban karamar hukumar ya bukaci mutane su guji aikata wani abu da ka iya tayar da zaune tsaye a lokacin zaben da ma bayan an kammala zaben. Shugaban APC na karamar hukumar Zaria, Abdu Ringo ya ce babu wata gwamnati da ta taba bayar da kwangila na N1.1 biliyan tun 1999 da aka dawo mulkin demokradiyya. "Idan muna son wadandan ayyukan su cigaba, ya zama dole mu zabi jam'iyyar APC domin mu cigaba da more romon demokradiya." Ya ce idan gudanar da ayyuka ke sanya a sake zaben shugabanni, tabbas jam'iyyar APC ta cancani a sake zaben ta.
No comments:
Write Comments