Tuesday

Home Abinda ka shuka: Gwamnonin Najeriya guda 2 da suka gagara lashe zaben Sanata
Tun bayan kammala kada kuri’u a babban zaben Najeriya daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu ne aka fara tattara alkalumman sakamakon zaben daga kowace rumfa, mazaba, karamar hukuma, jaha da ma kasa baki daya, tare da kidayarsu.Kuma zuwa yanzu an fara samun tabbatattu kuma sahihan sakamakon zabukan da suka gudana, inda yan siyasa da dama da suka tsaya takara sun fara sanin matsayinsu, walau sun samu nasara ko kuma akasin haka.

KU KARANTA: Sakamakon zabe: Tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka lashe zaben Sanata

Dankwambo da Ajimobi
Sai dai a mataki na bambarakwai, ba kamar yadda aka saba gani ba, an samu wasu manyan gwamnoni guda biyu da suka riga rana faduwa a zaben, inda wadannan gwamnoni dake rike da madafan iko a yanzu haka suka yi kokarin haurawa zuwa majalisar dattawa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito daga cikin gwamnonin nan akwai gwamnan jahar Gombe, Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, gwamna daya tilo na jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso gabas, da takwaransa na jahar Oyo, Gwamna Abiola Ajimobi, surukin gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

A jahar Gombe, dan takarar jam’iyyar APC, Saidu Alkali ne ya tika Gwamna Dankwambo da kasa a gogoriyon wakiltar mazabar Gombe ta Arewa a majalisar dattawa, inda Alkali ya samu kuri’u 152,546 Dankwambo kuma ya samu 88,016, kamar yadda baturen zabe Farfesa Umar Gurama ya bayyana.

Shi kuwa gwamnan jahar Oyo, Abiola Ajimobi wanda ya taba zama Sanatan Oyo ta kudu kafin ya zama gwamna, ya gamu da tasgaro a kokarinsa na sake komawa majalisar dattawan, inda dan takarar PDP, Kola Balogun ya nanashi da kasa da kuri’u 105,720, yayin da gwamnan ya samu 92,218.
No comments:
Write Comments