Tuesday

Home Abu na farko da zan fara aikatawa bayan na d'are karagar mulki :- cewar Atiku
Atiku ya sake bayar da wannan tabbaci ne a jiya Litinin cikin jawaban sa ga magoya baya yayin taron sa na yakin zabe da ya gudanar a harabar filin wasanni na Adokiye Amiesimaka da ke birnin Fatakwal na jihar Ribas.
Atiku  money

Wazirin Adamawa tare da abokin takarar sa, Peter Obi da kuma sauran jiga-jigai na jam'iyyar PDP, sun sha alwashin riko da doka tare da yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan da'a a kowane yanayi yayin da suke rike da akalar jagorancin kasar nan.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit ta ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma sha alwashin dawo da martabar birnin Fatakwal muddin ya yi nasara a babban zabe da za a gudanar a ranar Asabar mai gabatowa.
Cikin jawaban su duba da yadda gwamnatin jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi riko na sakainar kashi wajen tafiyar da al'amurran kasar nan, Atiku da abokin takarar sa sun sha alwashin dawo da duk wata martaba ta inganci a kasar nan.
No comments:
Write Comments