Tuesday

Home APC ta yi mana rashin adalci a jiharmu - cewar gwamnan zamfara
Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari yace jam’iyyar APC bata yiwa al’umar Zamfara magoya bayan jam’iyyar apc  adalci ba

- Abdul-aziz Yari ya yi wannan furucin ne a cikin wata hira da "yan jarida a birnin Abuja

- Gwamnan yace "duk da ran su ya baci, mun yafe wa APC rashin adalcin da ta yi mana"


Cikin bidiyon dai Yari ya rika jawo  ayoyi daga cikin kundin tsarin mulkin Najeriya da ya ce sun nuna halascin zaben fidda gwanin na APC a jihar.

Bayan nan kuma ya sake bads misali da yadda aka bayyana sunan Shuga Buhari a takarar shugaban kasa, a ka ce an yards shi ne dan takarar APC.

ya ce duk da haka an bi kananan hukumomi da jihohi an yi zaben tabbatar da Buharin, sannan aka koma Abuja aka tabbatar dashi.

A kan haka ya bayyana cewar ashe kenan su ma abin da suka yi a Zamfara daidai ne.

Gwamnan wanda tenure sa ke karewa cikin watan May, ya yi wa jihar sa fatan alheri da kuma addu'ar samun shugabanni nagari anan gaba.
No comments:
Write Comments