Thursday

Home Ba karamin kuskure bane sake zabar Buhari A ranar asabar mai zuwa :- Cewar Alhaji sani ibrahim
Ko’odinatan Yaqin Neman zaben dan takarar shugaban qasa a inuwar jamiyyar PDP na yankin Funtuwa Alh. Salisu Ibrahim Munafata ya bayyana cewar, idan yan Nijeriya suka sake yin kuskuren zabar Shugaban qasa Muhammad Buhari uqubar yunwa, talauci da kuma rashin tsaro da suka addabi qasar nan, musamman na yan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas da kuma satar jama’a sai sun fi na baya.A hirar sa da LEADERSHIP A Yau a Kaduna, Munafata ya ce,” ba fata muke yi ba, amma a irin wannan riqon Sakainar Kashin da gwamnatin Buhari take yi mana, idan mutane suka sake kuskuren da suka yi na baiwa gwamnatin Buhari dama ta shekaru hudu, sai dai muce Inna lillahi Wa’inna Ilaihirraji’una, muna fatan Allah ya canza mana da Atiku Abubakar a 2019.”
Ya ce, “ abin kunya ne a ce, Buhari ya kasa kawo qarshen rashin tsaron da ya addabi Nijeriya , musamman a yankin Arewa maso gabas, babbu shakka sojoji suna iya qoqarin su amma gudunmawar da ya kamata gwamnatin Buhari ta basu ba ta yi kuma hakan ya nuna a zahiri gwamnatin Buhari ta gaza, siyasa kawai take yi da yaqin na yan ta’adda na cewar an rage kaifin yan qunguyar a yankin na Arewa maso gabas”.
A cewar sa, “ wasu yan Nijeriya sun saki Allah suna kallon Buhari ya yi masu aikin da Allah zaiyi, sai Allah ya zare hannun sa ya barsu da Buhari, masali yau lamarin sace mutane ya addabi yankin Arewa maso Yamma har da jihar sa Katsina, lala cewar tsaro a wannan lokacin yafi a baya, kada mu yaudari kanmu, lokaci ya yi da yan Nijeriya zazu zabi Atiku duk da cewar shi ba soja bane, amma ya qware wajen janyo qwararrun masana da suka san harkar tsaro.”
A fannin tattalin arzikjn qasa, Munafata ya ce, “Atiku ya yi fice ba wai a Nijeriya kawai ba har da fadin duniya domin dan kasuwa ne shahararre ya san yadda zai farfado da tattalin arzikin Nijeriya dake gab da durqushewa a qarqashin gwamnatin Buhari, da Buhari ya zamo shugaban qasa, kasuwannninmu sun koma tamkar fagen fafata yaqi, yunwa ta da mu mutane musamman takakawa, inka lisafa jihohi uku zuwa hudu a Arewa dake fama da takauci da rashin tsaro sai ka saka har da Katsina, musamman Daura mahaifar sa, domin duk fadin Katsina, babu garin da keda yan Garuwa kamar Daura domin babu wani abinda ya yiwa yan garin na tallafawa rayuwar su, a matsaykn sa na shugaban qasa da ya fito daga Daura, tunda Buhari baban mu, yayan mu kuma danmu ya gaza, me zai sanya mu canza shi da mutumin Adamawa ba Atiku domin munada yaqinin zai kai qasar nan da kuma qasar ga tudun mun tsira”.
Munafata ya yi nuni da cewa,” a farkon ahekaru biyu na mulkin PDP a baya can, ta yi abibda in za’a baiwa APC shekaru 16 a qara mata wasu shekaru 16, ba za ta yi shi ba.”
A qarshe ya ce,” abu biyu muke buqata idan Buhari yaje yaqin neman zabe Katsina gobe Alhamis, ya nemi gafarar Katsinawa na tallata masu Gwamana Masari da ya yi a 2015, domin bai yiwa Katsina komai ba, sai ayyukan PDP yake bi yana yiwa fenti, na biyu kuma, kada ya daga hannun Masari.”

SOURCE LEADERSHIP.NG
No comments:
Write Comments