Tuesday

Home Bisa tsautsayi : Jami'in Custom Ya kashe wani matashi har lahira : Hukumar Custom tayi karin Haske akan lamarin.
Bisa tsautsayi : Jami'in Custom Ya kashe wani matashi har lahira : Hukumar Custom tayi karin Haske akan lamarin.

Hukumar fasa kaurin, ta fitar da jawabi na musamman game da kisan da ake zargin wani jami’in ta da yi. An rasa rai ne lokacin da aka yi kokarin tare da wasu kaya da aka shigo da su a boye cikin Najeriya a yankin Shagamu da ke kudu.Mai magana da yawun bakin hukumar, DC Joseph Attah, ya bayyana cewa wannan rashi da ak yi bai yi masu dadi ba, amma yace yanayi ne na aiki ya zo da wannan abin takaici, inda har aka samu wani jami’i ya samu rauni a sakamkon haka.

Joseph Attah ya fitar da jawabi yana karyata cewa jami’an hukumar sun harbe wani fasinjan mota ne a kan hanya Ijebu-Ode da ke cikin garin Sagamu a jihar Ogun. Hukumar tace tsatsayi ne ya rutsa da wannan matashi da aka kashe.

Attah yace an samu bacin rana ne linzamin bindigar ta kubce aka harbi wani yaro da ke yi masu aiki. Babban jami’in yace wanda aka harbe din ba fasinjan mota bane, asali ma yake cewa wani Yaro ne da yake taya jami’an hukumar aiki.

Mai magana a madadin hukumar yake cewa wasu fasinjojin motar da su ke dauke da kaya ne su ka dauki bidiyon abin da ya wakana, a karshe su ka kama hanya su kayi tafiyar su, wanda kowa ya dauka cewa wani na cikin motar aka kashe.

Hukumar ta nuna takaicin ta na wannan rashi da aka yi inda ita kan ta wani karamin jami’in ta mai suna Destiny Onembamho yake faman jinya a halin yanzu bayan kubcewar dalmar. Yanzu dai ana gudanar da bincike a kan abin da ya auku.
No comments:
Write Comments